To fa! An yi wa sarkin Kano asiri da mujiya

To fa! An yi wa sarkin Kano asiri da mujiya

Al'ummar Lokon Kamfa dake unguwar Mandawari a cikin birnin Kano ne suka ga wannan mujiya da laya tana shawagi a cikin dare, bayan da Allah ya sa wannan mujiya ta fado an samu wadanda suka bude layar suka ga abin da ke ciki.

Zuma Times Hausa ta samu ganin wannan rubutu dake cikin layar, wanda aka gano rubutun wata aya ce a cikin Alkur'ani mai girma, aya ta 65 cikin suratul Yasin.

A cikin ayar an bude girman munjayen da yake cikin ayar, inda aka ga an rubuta sunan Sunusi Lamido Sunusi, Sarkin Kano mai ci.

To fa! An yi wa sarkin Kano asiri da mujiya
To fa! An yi wa sarkin Kano asiri da mujiya

KU KARANTA: Osinbajo ya tattaro jami'an tsaro zuwa taro

Legit.ng ta samu labarin cewa lallai da ake cewa, biri ya so ya yi kama da mutum. Domin in kun tuna a kwanakin baya bayan nan, mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na ll ya fuskanci barazana mai tsanani da har aka fara wani bincike a kansa, sakamakon wasu korafe korafe da aka ce an yi game da yadda yake tafiyar da harkokin sa na mulki.

Allah dai ya kara kare imanin mu da mutuncin mu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel