Kunji abunda gurbataccen kalanzir yayi wa wata mata

Kunji abunda gurbataccen kalanzir yayi wa wata mata

- Wata mata mai shekaru 40 ta gamu da ajalin ta a sakamakon amfani da ta yi da wani kalanzir da aka yi wa algus.

- Lamarin wanda ya auku a kauyen Ozoro da ke karamar hukumar Isoko North a jahar Delta ya sanya mutanen yankin a cikin alhini.

Rahotanni sun bayyana cewa matar mai suna Grace ta yi yunkurin zuba kalanzir din ne a cikin fitila, sai fitilar ta yi bindiga ta sanya wa jikin ta wuta.

NAIJ.com ta samu labarin ta yi ta kurma ihu domin makota su kawo mata dauki, amma da yake abun ya zo da ajali, kafin su iso, wutar ta ci karfin ta.

Kunji abunda gurbataccen kalanzir yayi wa wata mata

Kunji abunda gurbataccen kalanzir yayi wa wata mata

KU KARANTA: Wani mutun ya cire wa wata mata hakori saboda Burodi

An garzaya da ita zuwa asibiti, inda ta ce ga garinku nan.

Hukumar man fetur ta kasa NNPC dai ta dade ta na yi wa mazauna jahar Delta da Edo gargadi game da saye da amfani da gurbataccen kalanzir.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar zana jarabawar Post UTME

Jami'ar Legas ta bada sanarwar ranar da dalibai zasu zana jarabawar Post UTME
NAIJ.com
Mailfire view pixel