Gwamnatin Buhari ta bayyana yadda take kashe N6 biliyan duk wata akan matasa

Gwamnatin Buhari ta bayyana yadda take kashe N6 biliyan duk wata akan matasa

- Yayin da wasu jihohin Najeriya ke korafi kan shirin samar da aikin wucin gadi da gwamnatin kasar ta kirkiro dashi watau N-Power ke tafiyar hawainiya

- Yanzu haka jami’an kula da shirin na gudanar da wani ziyarar gani da ido, inda suka isa jihar Taraba inda anan ma ake kokawa.

Gwamnatin kasar dai tace ta na kashe zunzurutun kudin daya kai Naira biliyan shida a kowani wata kan shirin aikin wucin gadin da take yi na N-Power, da zammar magance rashin aikin yi a tsakanin matasa.

Yayin ziyarar gani da ido na yadda shirin ke gudana a jihar Taraban, hadimin shugaban kasa kan harkokin samar da ayyukan yi, Mr Afolabi Inmokhide ya yaba da yadda matasa ke son runguman shirin na N-Power wanda yace an kirkiro da shirin ne da zammar magance zaman kasha wando.

Gwamnatin Buhari ta bayyana yadda take kashe N6 biliyan duk wata akan matasa

Gwamnatin Buhari ta bayyana yadda take kashe N6 biliyan duk wata akan matasa

KU KARANTA: Wani na kusa da Jonathan ya caccaki dattijan Arewa

NAIJ.com ta samu labarin cewa hadimin ya shawarci matasan dake cin gajiyar shirin da su tabbatar sun yi adashen gata da wani abu daga cikin Naira dubu talatin (N30,000), din da ake basu na alawus din wata-wata.

Yace ,’’ munzo ne muga yadda shirin ke tafiya kamar sauran jihohi, kuma manufar wannan shiri shine na samar da ayyukan yi inda wasu za’a tura su makarantu ,da wasu wurare da kuma harkar noma kamar yadda muka tarar, don haka ya kamata a maida hankali domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
‘Yan majalisar tarayya na kudu maso gabas sun yi Allah wadai ga kalaman soji a kan kungiyar IPOB

‘Yan majalisar tarayya na kudu maso gabas sun yi Allah wadai ga kalaman soji a kan kungiyar IPOB

‘Yan majalisar tarayya na kudu maso gabas sun yi Allah wadai ga kalaman soji a kan kungiyar IPOB
NAIJ.com
Mailfire view pixel