Kwallon kafa: Kungiyar Arsenal ta rasa gurbin gasar zakarun Turai

Kwallon kafa: Kungiyar Arsenal ta rasa gurbin gasar zakarun Turai

- A karon farko Arsenal ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta badi duk da doke Everton 3-1 da ta yi a ranar Lahadi a wasan karshe na gasar Premier

- Arsenal wadda sau 20 tana zuwa gasar zakarun Turai din ta kammala wasannin Premier ta bana a mataki na biyar, bayan da ta yi wasanni 38 ta ci 23 ta yi canjaras 6 aka doke ta sau 9

A karon farko Arsenal ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta badi duk da doke Everton 3-1 da ta yi a ranar Lahadi a wasan karshe na gasar Premier.

Arsenal wadda sau 20 tana zuwa gasar zakarun Turai din ta kammala wasannin Premier ta bana a mataki na biyar, bayan da ta yi wasanni 38 ta ci 23 ta yi canjaras 6 aka doke ta sau 9.

Kungiyar da ke birnin Landan ta ci kwallo 77 aka zura mata 44, yayin da ta hada maki 75, wanda hakan ke nufin Arsenal za ta buga gasar kofin Europa na badi kenan.

Kwallon kafa: Kungiyar Arsenal ta rasa gurbin gasar zakarun Turai
Kwallon kafa: Kungiyar Arsenal ta rasa gurbin gasar zakarun Turai

KU KARANTA: Kasuwar kwadi ya girma a Hadeja

Legit.ng ta samu labarin cewa Chelsea ce ta lashe kofin bana kuma na shida jumulla sai Tottenham ta biyu Manchester City ta uku, inda Liverpool ce ta hudu.

Kungiyoyi uku da suka kasa kai bantensu a gasar bana sun hada da Hull City da Middlesbrough da Sunderland, wadanda za su koma buga Championship a badi.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel