An yi Jana’izar uwargidan Malam Aminu Kano

An yi Jana’izar uwargidan Malam Aminu Kano

- An gudanar da Jana'izar uwargidan marigayi Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a yau Litinin

- Hajiya Shatu ta rasu a jiya Lahadi, 21 ga watan Mayu bayan tayi fama da doguwar jinya a birnin Kano

An gudanar da Jana'izar uwargidan marigayi Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a yau Litinin, 22 ga watan Mayu.

Hajiya Shatu ta rasu a jiya Lahadi, 21 ga watan Mayu bayan tayi fama da doguwar jinya a birnin Kano.

KU KARANTA KUMA: Matan Chibok: Wani Sanata ya bayyana abin da ya sa aka yi musanya da ‘Yan ta’adda

Marigayiyar ta rasu tana da shekaru 89 a duniya, ta kuma rasu ta bar jikoki goma sha biyar a duniya.

An yi Jana’izar uwargidan Malam Aminu Kano
Marigayiya Hajiya Shatu Aminu Kano

Ta rasu bayan shekaru 34 da rasuwar mijinta Malam Aminu Kano shahararen dan siyasa a arewacin Najeriya wanda ya kafa jam’iyyar NEPU ta masu ra’ayin rikau na yan mazan jiya.

An yi Jana’izar uwargidan Malam Aminu Kano
Al'umma sun taru a gurin Jana’izar uwargidan Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a birnin Kano

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya (INEC) Farfesa Attahiru Jega ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kamar maza.‎

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An saki 'Yan matan makarantar Chibok da aka sace shekaru ukku da ya gabata

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel