367

USD/NGN

Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019, inji fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019, inji fadar shugaban kasa

- Shekaru biyu da hawan shugaba Buhari mulki, ya fara samun suka da soyayya kan batun 2019

- Ana jinyar shugaba Buhari kusan duk shekarar nan

- Fadar Shugaban kasa tace shine ma zai lashe zabe kuma zayyi takara

Mataimakin Shugaba Buhari kan harkokin manema labarai, Malam Garba Shehu, yace ko da a yau aka gudanar da zaben shugaban kasa, toh lallai Buhari ne zai lashe zaben, domin a cewarsa, 'yan Najeriya na farin ciki da yadda salon mulkin Buharin yake. Ya dai fadi hakan ne, a yau da safe a gaban manema labarai.

Buhari ne zai lashe zaben 2019, inji Fadar Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Malam Garba Shehun, ya kara da cewa, ai ma duk soki-burutsu ne na siyasa jam'iyyar adawa take yi, domin kayen da suka sha a shekaru biyu da suka gabata a shekarar 2015.

An dai shafe shekaru biyu kenan tun da jam'iyyar APC ta amshi mulki, kuma shugaba Buhari na jinya a asibiti a Turai, kusan duk tsawon wannan shekara, bai kuma ce zayyi ko bazai yi takara ba a zabe mai zuwa.

Related news
Tsagerun Neja Delta sun mara wa shuagabn Biyafara baya akan hana zaben Anambara

Tsagerun Neja Delta sun mara wa shuagabn Biyafara baya akan hana zaben Anambara

Tsagerun Neja Delta sun mara wa shuagabn Biyafara baya akan hana zaben Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel