Hotunan bindigu 440 da aka kama a jihar Legas

Hotunan bindigu 440 da aka kama a jihar Legas

- Hukumar kwastam ta kama wasu dimbin makamai da suka hada da bindigu 440 da alburusai

- Hukumar ta bayyana cewar makaman sun fito ne daga kasar Turkey, amma a kasar Amurka da Italiya aka kera su

A ranar Talata 23 ga watan Mayu ne jami’an hukumar kwastam ta kama wasu dimbin makamai da suka hada da bindigu 440 da alburusai a tashar jirage na jihar Legas.

Hukumar ta bayyana cewar makaman sun fito ne daga kasar Turkey, amma a kasar Amurka da Italiya aka kera su, shugaban hukumar ta kwastam Hamid Ali ne ya bayyana haka ta bakin Kaakakin hukumar, Monday Abue

KU KARANTA: An rufe jami’a bayan Sojoji sun lakaɗa ma ɗalibai da malamai duka (Hotuna da Bidiyo)

Abue yace “Bindigu ne masu hadari sosai, wadanda ake kira Pump-Action, mun kama su ne a cikin simintin POP, kuma zuwa yanzu mun kama wani dake da hannu cikin safarar makaman, amma ba zamu bayyana shi yanzu ba har sai mun kammala bincike.”

Hotunan bindigu 440 da aka kama a jihar Legas
Hotunan Makaman

Shi kuwa Kaakakin hukumar kwastam reshen tashar jiragen ruwa na Legas, Uche Eiesieme ya bayyana yawan makaman dalla dalla, wadanda suka hada da: Bindigu kirar Black Tornado mai baki daya guda 100, Bindiga kirar Silver Magnum mai baki daya guda 75, Bindiga kirar Altar pump guda 50, sai bindiga kirar Black guda 215 tare da dimbin alburusai.

Hotunan bindigu 440 da aka kama a jihar Legas
Hotunan makaman

Bugu da kari, shugaban hukumar ya bayyana cewar daga kasar Turkiyya aka yi odar makaman, amma asalinsu a kasar Amurka da kasar Italiya aka kera su, kamar yadda Legit.ng ta kalato.

Hotunan bindigu 440 da aka kama a jihar Legas
Hotunan bindigun

Idan ba’a manta ba, a watan Janairun bana ma hukumar ta kwastam ta kama bindigu guda 661 a tashar jirage na Legas.

ga sauran hotunan:

Hotunan bindigu 440 da aka kama a jihar Legas
Sunduki

Hotunan bindigu 440 da aka kama a jihar Legas
Simintin POP

Hotunan bindigu 440 da aka kama a jihar Legas
Hotunan bindigun

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tattakin yaki da rashawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel