Kudin Najeriya Naira ba tada amfani a kasar waje – Tsohon Ma’aikaci CBN

Kudin Najeriya Naira ba tada amfani a kasar waje – Tsohon Ma’aikaci CBN

Wani mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailafia, ya bayyana cewa da yiwuwan Naira ta zama ba amfani a wajen Najeriya kamar da.

Mailafiya ya tuna cewa a shekarun baya, ana amfani da kudin Najeriya a Landan, Makkah da Madina.

Yayi kira ga gwamnatin tarayya ta dau matakai da zai sanya Naira tayi amfani a wajen Najeriya.

Kudin Najeriya Naira ba tada amfani a kasar waje – Tsohon Ma’aikaci CBN
Kudin Najeriya Naira ba tada amfani a kasar waje – Tsohon Ma’aikaci CBN

Yace: “ A shekarun 70’s, yan Najeriya suna amfani da Naira a Landan. Bal ma musulmai na amfani da shi a Makkah da Madina inda suke iya saya da sayarwa.

“Abun ya lalace yanzu da har a kasan Benin, ba’ a amince da Naira ba. Ya kamata mu gyara karfin sayarmu.

“CBN ta yi gaskiya akan zata take samar da wasu dokokin shiga da ficen kudi da kuma yadda take bibitan sauran bankuna.

KU KARANTA: Majalisar dokoki ta dakatad da bincike sarkin Kano

“Wannan zai taimaka wajen wajen tabbatar da cewa bankunan zasuyi abinda ya kamata wajen farfado da tattalin arzikin kasa.”

“Idan akayi hakan kuma akan fadada yadda ake samun kudin mu, zai saukaka nauyin da Naira keyi kuma zai karfafa shi.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel