366

USD/NGN

Obasanjo, Osinbajo da sauran su sun tattauna a kan Biyafara bayan shekaru 50 a Abuja

Obasanjo, Osinbajo da sauran su sun tattauna a kan Biyafara bayan shekaru 50 a Abuja

- Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo da mutane da dama sun halarci taron tattaunawa a kan yakin basasa bayan shekaru 50

- Rahotanni sun nuna cewa ce ba’a taba irin wannan taron ba

- Wannan ne karo na farko da aka shirya wannan taro ba tare da wani abu ko wani mutun ya dakatar da shi ba

A yanzu haka mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo da mutane da dama na nan a zaune a cibiyar Musa Yar’adua dake Abuja domin tattaunawa a kan yakin basasa na biyafara bayan shekaru 50.

NAIJ.com ta tattaro cewa wadanda suka zauna muhawaran sun hada da shugaban kungiyar Inyamurai wato Ohanaeze Ndigbo John Nnia-Nwodo, Pat Utomi da kuma shugaban taron, Mohammed Jada.

Da yake magana a gurin taron, Innocent Chukwuma na gidauniyar Ford wadanda suka hada taron tare da gidauniyar Shehu Musa Yar’adua sun ce ba’a taba irin wannan taron ba.

KU KARANTA KUMA: Kalli ‘yar Najeriya da ta yi zarra a gasar musabakar al-Kur’ani ta duniya (HOTUNA)

Obasanjo, Osinbajo da sauran su sun tattauna a kan Biyafara bayan shekaru 50 a Abuja

Obasanjo, Osinbajo da sauran su a gurin taron da aka gudanar a babban birnin tarayya

Chukwuma ya ce: “Wannan ne karo na farko da aka shirya wannan taro ba tare da wani abu ko wani mutun ya dakatar da shi ba.

KU KARANTA KUMA: Za’a ci gaba da bincikar sarkin Kano

"Babu shakka dukkan mutane da suka halarcin taron sun ji dadin kasancewa a gurin taron har ma da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo", cewar Chukwuma.

Ya kara da ba da shawarar cewa a ware wata rana don tunawa da abubuwan da suka faru a lokacin yakin basasa na 1967.

“Wannan na da matukar muhimmanci saboda ba’a koyar da tarihi a makarantun mu yanzu,” cewar sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Related news
Rundunar yan sandan jihar Bayelsa sun cafke yaro dan shekara 10 da ke fashi da sata

Rundunar yan sandan jihar Bayelsa sun cafke yaro dan shekara 10 da ke fashi da sata

Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami
NAIJ.com
Mailfire view pixel