367

USD/NGN

A ranar Asabar ne za a soma azumi a kasar Saudiya

A ranar Asabar ne za a soma azumi a kasar Saudiya

- Hukumomin Saudiya da Daular Larabawa sun sanar cewa za su fara azumin bana a ranar Asabar nan mai zuwa

- Sanarwar ta biyo bayan rashin ganin jinjirin watan Ramadan a ranar Alhamis

- Kasar Lebanon ma ta bayyana ranar asabar a matsayin ranar da zata tashi da azumin Ramadan

Hukumomin kasashen Saudiya da Daular Larabawa sun bayyana a ranar Asabar, 27 ga watan Mayu cewa za su fara azumin watan Ramadan bayan kasa ganin jinjirin watan a yau Alhamis, 25 ga watan Mayu.

Sanarwar da hukumomin kasashen biyu suka bayar ta nuna cewar ba a ga jinjirin watan Ramadan a ranar Alhamis ba, saboda haka watan Sha'aban zai cika 30 a ranar Juma’a, 26 ga wata Mayu kuma ranar Asabar za ta kasance daya ga watan Ramadan.

Kasar Lebanon ita ma ta bayyana ranar asabar a matsayin ranar da za a tashi da Azumin Ramadan a kasar.

Zuwa yanzu babu sanarwa da ta fito daga kasar Iran.

KU KARANTA KUMA: Za’a fara neman watan Ramadan ranar Juma’a – Inji Sultan

A Najeriya tun ranar Laraba, 24 ga watan Mayu ne mai girma Sarkin Musulmi ya bayar da umurnin fara dibon watan na Ramadan.

Azumin watan Ramadan, yana cikin shika-shikan Musuluci kuma al’ummar Musulmi sukan kauracewa ci da sha da saduwa da iyali tun daga fitowar al fijir har zuwa faduwar rana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon direban Bishof David Abioye wanda ya karbi musulunci yayin da ya yi murabus da cocin Living Faith Church

Related news
Beraye da wasu Kwari ne suka tafka gagarumar barna a ofishin shugaban kasar

Beraye da wasu Kwari ne suka tafka gagarumar barna a ofishin shugaban kasar

Beraye da wasu Kwari ne suka tafka gagarumar barna a ofishin shugaban kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel