Tarzoma a Bauchi: An kama dalibai 32 masu hannu a rikicin COE Kangere

Tarzoma a Bauchi: An kama dalibai 32 masu hannu a rikicin COE Kangere

- An kama wasu dalibai 32 wandanda ake zargi suna da hannu a cikin rikicin Kwalejin Ilimi ta jihar akan daga zaben kungiyar dalibai (SUG) na makarantar.

- A cewar mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda reshen jihar Bauchi, SP Haruna Mohammed, rikicin dai ya samo asali ne bayan da kungiyar ‘daliban kwalejin ta gudanar da zabenta, inda aka samu rashin jituwa tsakanin ‘daliban game da sakamakon zaben da aka samu.

Legit.ng ta samu labarin cewa ya ce an daga zaben ne saboda yana neman sabawa dokokin makarantar saboda banbancin fadaci-addini da aka fara kawowa a harkar zaben.

A yanzu haka, Gwamnatin jihar Bauchi ta bayar da umarnin rufe Kwalejin Ilimi dake garin Kangere, a sanadiyar rikicin da aka samu tsakanin ‘dalibai da jami’an tsaro, wanda yayi sanadiyar raunata ‘dalibai da dama.

Tarzoma a Bauchi: An kama dalibai 32 masu hannu a rikicin COE Kangere
Tarzoma a Bauchi: An kama dalibai 32 masu hannu a rikicin COE Kangere

kwamishinan yada labarai Alhaji Abdullahi Idris, ya ce ganin cewa ‘daliban zasu yi rikici yasa aka hanasu yin zaben ranar Talata, jiya Laraba kuma ‘daliban suka fara tayar da hankali, har ta kai ga fita wajen makaranta da zuba duwatsu akan hanya har kusan wani shingen sojoji, da zummar hana motoci wucewa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel