Najeriya Batta da makoma mai kyau, inji Kungiyar Kabilar Igbo

Najeriya Batta da makoma mai kyau, inji Kungiyar Kabilar Igbo

- Kabilar Ibo sun taba ballewa daga Najeriya suka kafa kasar Bayafara

- An yi bikin cikar Biafra shekara 50 da kafuwa

- Ohanaeze ita ce kungiya mai magana da yawun kabilar Ibo

An yi taron cikar kafa kasar Biafra da ta ruguje a Abuja, mahankalta na kallon samarin Ibo a matsayin masu rajin son dawo da wannan kasa, tun bayan yakin basasa da aka kwashe shekaru biyu da rabi ana fafatawa.

Shugaban kungiyar kabilar Ibo, ya ce har yanzu Najeriya bata da wani ingatacciyar makoma, ba alkibla, babu kuma shiri na ina aka dosa.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai zamo shugaban kasar Najeriya na shekaru masu yawa

Najeriya Batta da makoma mai kyau, inji Kungiyar Kabilar Igbo

Najeriya Batta da makoma mai kyau, inji Kungiyar Kabilar Igbo

Shugaban kungiyar, Mr. Nwodo, yace "a harkar tattalin arziki, muna baya, a harkar ilmi, muna baya, a harkar ta'addanci, mune na uku a duniya, a batun yara a makaranta, munfi kowa, duk da cewa har mun kai mutum miliyan 182, amma bamu da wani katabus a duniya".

Ya kara da cewa, amma kuma hakan na iya zama wani damba na shirin nemawa kasa alkibla, domin alkalumma sun nuna cewa lallai akwai yiyuwar Najeriya ta zama babbar kasa nan bada dadewa ba.

A dai kiyasi, Najeriya zata zamo ta 20 a batun tattalin arziki nan ba da jimawa ba, a kuma wata ruwayar, nan da shekarun 2050, Najeriya zata zama ta uku a yawan al'umma a duniya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin jihar Filato a cikin shekaru 10

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin jihar Filato a cikin shekaru 10

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10
NAIJ.com
Mailfire view pixel