YANZU YANZU: Hukumar NSCIA ta sanar da fara azumin watan ramada a Najeriya

YANZU YANZU: Hukumar NSCIA ta sanar da fara azumin watan ramada a Najeriya

- Sakatare janar na kungiyar kula da harkokin addinin Musulunci NSCIA Ishaq Oloyede ne ya sanar da haka.

-Yace Sarkin Musulmi Abubakar zai sanar

- Gobe Asabar Musulman kasa Najeriya zasu tashi da Azumi

Musulman Najeriya zasu fara azumin watan Ramadana a ranar Asabar 27 ga watan Mayu, kungiyar kula da harkokin addinin Musulunci NSCIA ta sanar da hakan.

Sakatare janar na kungiyar kula da harkokin addinin Musulunci NSCIA Ishaq Oloyede wani farfesa ne ya sanar da haka, cewa an ga wata a gurere da dama a fadin kasar, sannan kuma cewa azumin Ramadana zai fara a ranar Asabar.

Yace Sarkin Musulmi Abubakar zai sanar ga manema labarai da jama’ar kasa a daren yau.

“Munayi wa musulman Najeriya da dukkan na duniya fatan Ramadan na gari mai cike da ibada,” cewar Oloyede."

Wani mai amfani da twitter Bashir Ahmad ma ya sanar da ganin wata a jihohin Sokoto, Lagos, Kano da sauransu

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Sheqau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Sheqau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram
NAIJ.com
Mailfire view pixel