Gwamna Tambuwal zai baiwa dalibai 20,000 kudin tallafin karatu

Gwamna Tambuwal zai baiwa dalibai 20,000 kudin tallafin karatu

- Kimanin dalibai dubu ashirin ne zasu amfana da tallafin karatu a Sakkwato

- Hukumar bada tallafin karatu tace a shirye take ta tallafa ma daliban

Kimanin dalibai dubu ashirin ne zasu samu kudin tallafin karatu daga gwamnatin jihar Sakkwato sakamakon kammala aikin tantancewa da gwamnatin ta gudanar, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Kwamishina ilimi na jihar Sakkwato, Alhaji Sahabi Isah Gada ne ya bayyana haka ga majiyar NAIJ.com, inda yace daliban su 20,000 sun hada da sabbin dalibai da tsofaffi.

KU KARANTA: An nemi Bunsurun Najeriya a Amurka sama ko ƙasa an rasa

“Mun gudanar da aikin tantancewa ga daliban namu, ta hakan ne zamu san adadin daliban da kuma yawan kudin da zamu biya.” Inji Kwamishinan

Gwamna Tambuwal zai baiwa dalibai 20,000 kudin tallafin karatu

Gwamna Tambuwal

Kwamishinan ya shaida cewa sun gudanar da irin wannan aikin tantancewa ga daliban jihar dake karatu a kasashen waje da suka hada da yankin Afirka, Turai da Amurka, ta hakan ne aka dawo da wasu dalibai 34 gida Najeriya don cigaba da karatukansu a jami’ar Baze mai zaman kanta a Abuja.

Kwamishina Gada ya bayyana cewa tun bayan da gwamnatin Aminu Tambuwal ta fara aiki, ta kashe dama da naira biliyan biyu wajen biyan tallafin kudin karatu ga daliban jihar.

Ya kara da cewa ko a kwanakin baya sai da gwamnatin jihar ta biya dalibanta dake Bangladesh da Sudan kudaden tallafinsu, sa’annan zata biya wadanda ke kasashen Uganda da Malaysia nan bada dadewa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin ma'aurata wanene mai lafi?

Source: Hausa.naij.com

Related news
Karanta yadda Yansanda suka rusa cibiyoyin matsafa da yan ƙungiyar Asiri a Legas

Karanta yadda Yansanda suka rusa cibiyoyin matsafa da yan ƙungiyar Asiri a Legas

Yansanda sun rugurguza matattaran matsafa guda 5 a jihar Legas (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel