NYSC zata tura yan bautan kasa gona

NYSC zata tura yan bautan kasa gona

Dirakta Janar na hukumar bautan kasa matasa, Birgediya Janar Sule Kazaure ya bayyana ranan Litinin cewa hukumar zata fara tura yan bautan kasa aikin noma.

Kazaure ya bayyana wannan ne a wata hira da manema labarai yayinda ya kai ziyara Sagamu, jihar Ogun.

Yace niyyar tura yan bautan kasa gona na cikin shirin aikin noman hukumar NYC.

Game da cewarsa, NYSC ta shirya wannan idan aka gama zaman horon makonni 3 da ke ciki a yanzu.

Yace jihar Bauchi, Oyo, Kebbi da Abuja ne za’a fara kaddamar da wannan shiri.

NYSC zata tura yan bautan kasa gona

NYSC zata tura yan bautan kasa gona

Zakuyi farin cikin cewa NYSC zata fara shirin aikin nomanta yayinda aka tura yan bautan kasa gona domin aiki.

“Tuni hukumar NYSC ta sam filaye a yanunan tarayya inda za’a fara ayyuka a Kwali, Bauchi, Oyo da Kebbi.

KU KARANTA: Maki kadan Buhari yaci, inji dan APC

“Bayan wannan kwanakin horon Batch ‘A’, zamu fara turasu gonaki domin aiki. Duk da cewan mun fara da jihohi 4 yanzu, zamu shiga wasu jihohi da lokaci."

Shugaban NYSC yayi kira gay an bautan kasa cewa kada su bata lokaci neman aikin gwamnati saboda babu, amma su shiga ayyukan hannu.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin jihar Filato a cikin shekaru 10

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin jihar Filato a cikin shekaru 10

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10
NAIJ.com
Mailfire view pixel