Ramadan: Yadda wani Alaranma ya karanta Suratul-Baqara a Raka’a daya

Ramadan: Yadda wani Alaranma ya karanta Suratul-Baqara a Raka’a daya

– A azumin bana an yi sallar da ba a taba yin irin ta ba

– Alaranma Badr Zafar ya karanta Suratul-Baqara a Raka’a guda

– Jama’a da dama sun samu rauni kafin a kammala sallar

A Masallacin Ar-Razzak da ke Birnin Landan an ga wata doguwar salla bana.

Wani saurayi ya saukewa jama’a izifi kusan 5 a tashi guda.

Sai da wasu su ka kassara a cikin wannan salla.

Ramadan: Yadda wani Alaranma ya karanta Suratul-Baqara a Raka’a daya
Wasu Bayin Allah na salla cikin Ramadan

A wani masallaci a Birnin Landan mun ji labarin cewa wani Alaranma mai suna Badr Zafar ya sauke Suratul Bakara mai ayoyi 286 a Raka’a guda a wata sallar tarawihi. Sai da aka dauki sama da minti 3 wajen furta ayar farko kurum watau Alif-Lam-Mim.

KU KARANTA: Abubuwan da ya kamata a daina lokacin Azumi

Sallar Ramadan
Jama’a sun samu rauni saboda tsawon wata sallar Tarawihi

Wadanda su ka halarci Sallar dai kamar yadda mu ka samu labari daga shafin Maniac Muslim, da dama sun samu rauni inda wasu su ka sare a gwiwa, akwai wani dan wasan kwallon Kwando dai da yanzu an ce ba zai iya kara komawa wasan ba.

Jiya kun ji cewa Jihohi 6 sun bayyana nawa Mahajjata za su biya domin sauke farali. Jihohin Neja, Nasarawa, Katsina, da kuma Jihohin Kano, Kaduna da Adamawa sun sun bayyana kudin kujerar hajjin bana wanda ya kera Miliyan daya da rabi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga kuma Jama'a na kuka a Najeriya [Bidiyo]

Asali: Legit.ng

Online view pixel