Toh fa: Kungiyar kabilar Igbo ta yi wa Kanu kashedi

Toh fa: Kungiyar kabilar Igbo ta yi wa Kanu kashedi

- Kungiyar matasa da dattawan yankin kudu maso gabas ta gargadi shugaban kungiyar ‘yan asalin mutanen Biyafara

- Kungiyar ta bayyana farin cikin ta cewa gwamnatin tarayya ta sake Kanu daga kurkuku

- Kungiyar ta kuma zargi shugabanin kudu maso gabas da suke gwamnatin nan da rashin tallafa wa yankin

Kungiyar matasa da dattawan na yankin kudu maso gabashin Najeriya wato SEYEF ta gargadin Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar ‘yan asalin mutanen Biyafara (IPOB) da ya daina karya wadancan yanayin belin da aka bashi.

Wannan kashedin dai ta kasance a cikin wata sanarwar da kungiyar ta yi bayan ganawar ta a Enugu baban birnin jihar, wanda darektan harkokin watsa labarai na kungiyar Maxi Ikechukwu K. Edwin ya sa hannu.

NAIJ.com ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana farin cikin ta cewa an sake Kanu daga kurkuku, amma duk da haka, kungiyar ta gargadi Kanu da ya kaurace wa duk abin da zai iya hada shi da gwamnati don kauce wa wani zagayen rikici da gwamnatin.

Toh fa: Kungiyar kabilar Igbo ta yi wa Kanu kashedi

‘Yan kungiyar Biyafara, IPOB

KU KARANTA: Biafra: Hukumar yan sanda tayi gargadi ga yan kungiyar IPOB

SEYEF ta kuma zargi shugabanin yankin da suke birnin tarayya ta Abuja cewa ba su yi isasshen abi da zai kawo wa yankin ci gaba ba.

SEYEF kuma ta yi Allah wadai da barazanar da gwamnatin tarayya take wa mataimakin shugaban majalisa sanata Ike Ekweremadu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shugaban kungiyar ‘yan asalin mutanen Biyafara (IPOB) ya samu yancin kansa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima

Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima

Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima
NAIJ.com
Mailfire view pixel