Ba na adawa da Buhari - Inji Bukola Saraki

Ba na adawa da Buhari - Inji Bukola Saraki

- Shugaban majalisar dattawa ya bayyana cewa shi baya adawa da shugaba Buhari

- Bukola Saraki ya ce sun biya ma shugaban kasar kashi casa’In cikin dari na bukatun da ya gabatar a gaban majalisar

Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya bayyana cewa shi baya adawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da shugaban kungiyar Izala, Sheik Sani Yahaya Jingir ya kai masa ziyarar ban girma a jiya Talata, 30 ga watan Mayu.

Ya kuma kara da cewa sun biya ma shugaban kasar kashi casa’In cikin dari (90%) na bukatun da ya gabatar a gaban majalisar.

KU KARANTA KUMA: Siyasa: Matsalolin da Jam’iyyar APC ke fama da su

Ba na adawa da Buhari - Inji Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa shi baya adawa da shugaba Muhammadu Buhari

A wani al’amari makamancin wannan NAIJ.com ta rahoto cewa shugaban jam'iyyar APC Chief John Odigie-Oyegun, ya ce ba duk nade-naden mukamai ne suka farantawa jam'iyyarsa rai ba, ya kuma ce an sami rashin jituwa tsakanin mabiya bayan nade-naden.

KU KARANTA KUMA: Ka yi mun gani, sai dai...: ‘Yan adawa sun yabawa Shugaban kasa Buhari

Ya kuma ce a lokacin da suka hau mulki sun taras da barna da yawa daga PDP, da ma kuma abubuwan da basu hango ba, wadanda suka saka dan jan lokaci kafin a fara gani a kasa.

A karshe NAIJ.com ta kawo inda yace za'a ci ribar shukar da suke yi saboda sabon tsarin da gwamnati ta faro na kyautata rayuwar al'umma.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko Jama'a za su yarda a kifar da Gwamnatin Buhari

Source: Hausa.naij.com

Related news
Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10
NAIJ.com
Mailfire view pixel