Jami’an rundunar sojin ruwa sun kai farmaki ofishin ‘yansanda, mutane 3 sun mutu

Jami’an rundunar sojin ruwa sun kai farmaki ofishin ‘yansanda, mutane 3 sun mutu

A wani rahoto da dumi-duminsa da ga jihar Cross-Rivers, jami’an rundunar sojin ruwa sun kai farmaki a daren Talatan nan wani ofishin ‘yan sanda dake garin Calabar in da suka yi ta barin wuta ba kakkautawa.

Kamar yadda muka jiyo daga majiyar, Jami’an rundunonin tsaron biyu sun sami sabani ne bayan wani dan sanda ya tsayar da wani jami’in sojin ruwa da ya ki tsaya wa wutan hanya.

Jami’an rundunar sojin ruwa sun kai farmaki ofishin ‘yansanda, mutane 3 sun mutu

Jami’an rundunar sojin ruwa sun kai farmaki ofishin ‘yansanda, mutane 3 sun mutu

NAIJ.com ta samu labarin cewa duk da kwamishinan ‘yan sandan jihar da shugaban rundunar sojin ruwa na jihar sun sasanta lamarin, da karfe 8 din daren yau sai ga sojojin sun dawo dauke da makamai su kayi ta barin wuta a ofishin ‘yan sandan.

Wani mazaunin unguwan yace akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu inda har yanzu da muke rubuta wannan labari ofishin ‘yan sandan na nan yana ci da wuta.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta samar da magungunan yaki da cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta samar da magungunan yaki da cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira

An samar da magunguna 915,000 don yaki da cutar kwalara a Borno
NAIJ.com
Mailfire view pixel