Dalilan da suka sa aka samu Karin kudin kujerar aikin hajjin bana a Najeriya – NAHCON

Dalilan da suka sa aka samu Karin kudin kujerar aikin hajjin bana a Najeriya – NAHCON

- Hukumar aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana dalilan da suka sa aka samu karin kusan kashi 50 bisa dari a kudin kujerar aikin hajjin bana a kasar

- Shugaban hukumar NAHCON ya ce karin ya tsaya a 50% ne ma saboda rangwamen da gwamnatin kasar ta yi wajen yi wa maniyyatan canjin dalar Amurka

- Ya kara da cewa faduwar darajar Naira shi ne ginshiki na karuwar farashi, duk kuwa da rangwamen da gwamnatin kasar ta yi

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana dalilan da suka sa aka samu karin kusan kashi 50 bisa dari a kudin kujerar aikin hajjin bana a kasar.

A makon nan ne hukumar ta bayyana yawan kudaden kujera a bana wanda ya nuna kudin kujera mafi karanci shi ne sama da Naira miliyan daya da rabi.

Hakan dai ya sa wasu maniyyata da dama a Najeriya yanke kaunar sauke faralin a bana.

Dalilan da suka sa aka samu Karin kudin kujerar aikin hajjin bana a Najeriya – NAHCON
Hukumar aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON ta bayyana cewa faduwar darajar Naira shi ne ginshiki na karuwar farashi, duk kuwa da rangwamen da gwamnatin kasar ta yi

Shugaban hukumar ta NAHCON Alhaji Abdullahi Mukhtar Muhammad ya ce, karin ya tsaya a kashi hamsin bisa darin (50%) ne ma saboda rangwamen da gwamnatin kasar ta yi wajen yi wa maniyyatan canjin dalar Amurka.

KU KARANTA KUMA: Daga sama Buhari ke mulki - Femi Fani-Kayode

Ya kara da cewa, faduwar darajar Naira shi ne ginshiki na karuwar farashi, duk kuwa da rangwamen da gwamnatin kasar ta yi.

Shugaban hukumar aikin Hajji ta Najeriyar ya kara da cewa a wannan karo an samu raguwar Dala dari uku a kudin da alhazai ke biya na masauki da kuma kudin jirgi.

Legit.ng ta samu labarin cewa a bara maniyyata daga arewacin kasar sun biya Naira 998,248.92 a karamar kujera, wasu kuma sun biya Naira 1,047,498.92 na matsakaiciyar kujera, kana masu babbar kujera sun biya Naira 1,145,998.92.

Su kuma maniyyata daga kudancin kasar sun biya Naira 1,008,197.42, su kuma masu matsaikaiciyyar kujera kuma sun biya N1,057,447.42, inda masu babbar kujera suka biya Naira 1,155,947.42.

A bana an soke wannan tsarin kujeru daki-daki, inda aka mayar da shi na bai daya, kuma kowane maniyyaci zai biya abin da jiharsa ta kayyade.

A bana an tsayar da guzurin bai daya na dala 800 na Amurka.

KU KARANTA KUMA: Idan ka ji abin da ‘Yan Najeriya su ka yi asara a tsarin MMM sai ka yi kuka

Legit.ng ta tuna cewa shugabannin addini sun fara kira ga Gwamnatin tarayya da su shigo cikin lamarin domin samun yadda talaka zai samu rangwame, inda Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah Wa'Ikamatis Sunnah a Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi kira ga gwamnatin Najeriya ta bada tallafi na musamman domin sassauta kudin aikin hajjin bana, wanda al'umma da dama suka shiga damuwa domin tashin farashin kujerar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel