Dangote na biyan jihar Binuwe harajin N700,000,000 – Inji Gwamna

Dangote na biyan jihar Binuwe harajin N700,000,000 – Inji Gwamna

- Gwamnan jihar Binuwe Samuel Ortom yace Dangote na biyan haraji yadda ya kamata

- Dangote ya rarraba Babura masu kafa uku a Binuwe

Gwamnan jihar Binuwe Samuel Ortom ya bayyana cewar kamfanin Dangote dake garin Gboko na biyan harajin naira miliyan 700 ga gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da kamfanin simintin Dangote ya kaddamar da aikin rabon mashin mai kafa uku, da aka fi sani da suna adaidaita sahu a ga wasu al’ummomin jihar Binuwe a satin data gabata.

KU KARANTA: Jihar Sakkawato ta ɗauki nauyin mata 200 domin koyan likitanci

Dangote ya samu wakilcin mashawarcin sa Joe Makoju a wajen aikin rabon, inda gwamnan jihar tare da mukarrabansa suka halarci taron.

Dangote na biyan jihar Binuwe harajin N700,000,000 – Inji Gwamna
Gwamnan yayin kaddamar da rabon kekunan

Gwamna Ortom yayi alkawarin magance duk matsalolin da ake fuskanta musamman a sha’anin karba da biyan kudaden haraji a jihar, inda ya kara da cewa da ba don kamfanin Dangote ba, da bai san halin da tattalin arzikin kasar zata shiga ba.

Daga karshe Legit.ng ta ruwaito gwamnan na yaba ma kamfanin Dangote saboda samar da ayyukan yi ga matasan jihar, da kuma gudanar da ayyukan jin kai don amfanin al’ummar jihar.

Sauran aikace aikace da aka kaddamar sun hada da samar da wuta a kauyen Masaje, Ipav, Gaando, Mbayion, Igyula, Amua da Tsekutsa. Sa'annan an kaddamar da gina azuzuwa 14 a kauyukan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An mika yan matan Chibok ga maman Taraba

Asali: Legit.ng

Online view pixel