Dan majalisar da akayi garkuwa da shi ya samu yanci

Dan majalisar da akayi garkuwa da shi ya samu yanci

NAIJ.com ta samu labarin Wani dan majalisar wakilan tarayya dake wakiltar mazabar Sumaila/Takai na jihar Kano, Garba Durbunda ya samu yanci.

Anyi garkuwa da shi ne yayinda yake hanyar Abuja zuwa Kano a jiya 31 ga watan Mayu.

Game da cewan jaridar Premium Times, a yanzu haka dan majalisan na tare da iyakinsa.

“An sake shi ba tare da wani rauni ba kuma yana tare da iyalinsa. Na samu labarin cewa ashe bas hi suke nema ba saboda haka suka sakeshi ba tare da aman fansa ba” cewar Abdulrazak Namdas, mai magana da yawun majalisa.

Dan majalisar da akayi garkuwa da shi ya samu yanci

Dan majalisar da akayi garkuwa da shi ya samu yanci

Da farko NAIJ.com ta bada rahoton cewa anyi garkuwa da Mr. Durbunde yayinda yake tuki a hanyar Abuja zuwa Kano ranan Talata 30 ga watan Mayu misalin karfe 5 na yamma.

KU KARANTA: Babban fasto ya tunjuma cikin teku

Amma mai magana a yawun majalisa Abdulrazak Namdas, a lokacin yace bai samu labarin hakan ba.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta samar da magungunan yaki da cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta samar da magungunan yaki da cutar kwalara a sansanin 'yan gudun hijira

An samar da magunguna 915,000 don yaki da cutar kwalara a Borno
NAIJ.com
Mailfire view pixel