An birne dan sanda a raye bisa ga umurnin sarkin gargajiya a Legas

An birne dan sanda a raye bisa ga umurnin sarkin gargajiya a Legas

-Shin tsaro ta zama abinda ya zama ne a Najeriya

-Tunda har jami’in tsaro bai tsira ba inaga yaku bayi

Wani jami’in yan sandan Special Anti- Robbery Squad (SARS), Ikeja, Lagos mai suna, Musa Sunday, wanda aka alanta bacewarsa tun watan Nuwamban 2016, an tsince gawarsa cikin wata kabari a Ibeju Lekki a jihar Legas.

An gano cewa anyi garkuwa da jami’in ne kuma aka azabtar da shi kuma aka birneshi da ransa yayinda yake tsaron wata fili da ake rikici akai a Ibeju Lekki.

Sunday da wasu abokan aikinsa guda 4 ne aka tura gadin filin bisa ga umurnin shugabansu ba tare da ilimin shugaban sashen SARS ba da kuma kwamishanan yan sandan jihar, Mr, Fatai Owoseni.

An birne dan sanda a raye bisa ga umurnin sarkin gargajiya a Legas

An birne dan sanda a raye bisa ga umurnin sarkin gargajiya a Legas

Marigayi Sunday ya mutu yanada yara 4. An yi garkuwa da shi ne yayinda yake kokarin kare wani mutum daga hannun yan baranda.

KU KARANTA: An damke bokan da ke taimakon yan fashi

An samu rahoton cewa an hallaka wannan dan sanda ne da ilimin wani sarkin gargajiya a Legas wanda la’allla suna da baki cikin rikicin filin da akeyi.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Na shirya kare kaina a gaban kotu - Sanata Hamma Isa Misau

Na shirya kare kaina a gaban kotu - Sanata Hamma Isa Misau

Na shirya kare kaina a gaban kotu - Sanata Hamma Isa Misau
NAIJ.com
Mailfire view pixel