Kai dakikin gwamna ne - Dino Melaye ga Yahaya Bello

Kai dakikin gwamna ne - Dino Melaye ga Yahaya Bello

Sanata mai wakilatn Kogi ta yamma a majalisar dattawan tarayya, Dino Melaye, ya siffanta gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin dakikin gwamna na rashin iya biya albashin ma’aikatan jiharsa.

Dan majalisan yayi wannan bayani ne yayi yake magana kan rahoton da cewa gwamna Bello ya kaddamar da shirin tsigeshi daga majalisa.

A wata jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook yace:

“Yahaya Bello na amfani da kudi wajen biyan kamfanin jaridu domin bashi shafin waje na cewa ana kokarin tsige Dino Melaye.

Kai dakikin gwamna ne - Dino Melaye ga Yahaya Bello

Kai dakikin gwamna ne - Dino Melaye ga Yahaya Bello

“Abin ma dariya ya bani. Mutum dakiki irin Yahaya Bello wanda bai san yadda ake mayar da katin zabe daga Abuja zuwa Kogi ba ko kuma Edward Onoja wan aba a dadewa ba zai tafi gidan yari ne suke kokarin tsige sanata mafi kokarin 2016.

KU KARANTA: Naira na cigaba da samun galaba kan Dala

“Gwamnan da ya kasa biyan albashi ne yake daukan nauyin shirme. Nayi bayani kwanaki 2 da suka gabata cewa hakan zai faru. Ku tabbata cewa kun rubuta suna na da kyau a takardan INEC."

Dan majalisan ya maka gwamnan jihar, Yahaya Bello, a kotu kan rashin gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima

Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima

Matar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha tayi shar a sabon hotuna ita da yarta Fatima
NAIJ.com
Mailfire view pixel