• 365

    USD/NGN

Ramadan: An daure mutane 4 da suka ci abinci a rana tsaka

Ramadan: An daure mutane 4 da suka ci abinci a rana tsaka

- Wata kotu a kasar Tunisia ta daure wasu mutane hudu na tsawon wata guda a gidan yari

- Daure sun ya biyo bayan samun su da aka yi da laifin cin abinci a bainar jama’a alhalin ana azumin Ramadan

- A lokacin Azumi a kan rufe wuraren cin abinci a wasu sassa na Tunusia

Wata kotun kasar Tunisia ta daure wasu mutane hudu na tsawon wata guda a gidan yari bayan sun ci abinci a bainar jama’a da rana tsaka a yayin da ake azumin Ramadan.

An kama mutanen ne suna cin abinci da zukar taba a wani wajen shakatawa a birnin Tunis.

Bisa ga rahoto mai magana da yawun kotun Chokri Lahmar ya bayyana cewa mutanen hudu na da damar daukaka kara akan hukuncin cikin kwanaki 10.

KU KARANTA KUMA: Lai Muhammed yayi bayanin dalilan da yasa gwamnatinsu ke kin bin umarnin kotuna

Ramadan: An daure mutane 4 da suka ci abinci a rana tsaka

An daure mutane 4 da suka ci abinci a rana tsaka lokacin azumi a kasar Tunisia

A lokacin Azumi a kan rufe wuraren cin abinci a wasu sassa na Tunusia, koda dai babu wata doka a kundin tsarin mulkin kasar da ta haramtawa mutane cin abinci a bainar jama’a a lokacin azumi.

Batun dai na ci gaba da janyo ja-in-ja a kasa, inda yanzu haka wasu mutanen Tunisia suka shirya gudanar da zanga zanga domin kare ‘yancin wadanda ba su azumin Ramadan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo muku bidiyon yadda kayan marmari suka yi tsada a kasuwa saboda azumin Ramadan

Related news

Daga karshe, Buhari ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya ta hanyar sakon murya

Daga karshe, Buhari ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya ta hanyar sakon murya

Daga karshe, Buhari ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya ta hanyar sakon murya
NAIJ.com
Mailfire view pixel