Matashin kabilar Ibo mazaunin Amurka zai tsaya takarar shugabancin kasa

Matashin kabilar Ibo mazaunin Amurka zai tsaya takarar shugabancin kasa

- Wani matashin dan siyasa ya nuna ra'ayinsa na takarar shugabancin kasar nan daga Amurka

- Ya bayyana cewa zai furta hakan a taron 'yan Najeria mazauna Amurka

- Chris EMEJURU dai hamshakin dan kasuwa ne

A nasa hangen na yadda mulkin siyasa ya kamata ya kasance, dan kasuwa mazaunin Amurka yace nan da 'yan satuttuka zai mika kokon takararsa ga mabiya a wurin taron mutan Najeriya masu zama a kasashen waje, a karshen watan nan.

Emejuru dai yace shi ne zai ma kawo chanji a fagen siyasa, kuma shine zai gyara matsalolin da ke fuskantar kasa.

Yace yawon duniya da yayi ya bashi damar hangen yadda ayyukan ci gaba suke, da salon mulki daban-daban.

Matashin kabilar Ibo mazaunin Amurka zai tsaya takarar shugabancin kasa

Matashin kabilar Ibo mazaunin Amurka zai tsaya takarar shugabancin kasa

Matashin kabilar Igbon, ya ce: "Najeriya kasa daya ce, duba da kyawun arewa, martabar kudu, da hazakar 'yan kudu maso yamma, lallai zamu zamo masu nasara a matsayin kasa daya, kuma zamu baiwa Afirka da ma duniya baki daya misali".

KU KARANTA KUMA: Abin Murna: Buhari zai dawo bakin aikinsa nan da sati – Inji Kalu

A 'yan kwanakin nan dai, masu son su balle daga Najeroya 'yan kabilar Ibo ne, don haka zuwan kalaman nasa na nufin ba kowa ne yake sauraren 'yan ta-kife din ba. Sai dai karbuwarsa zata yiyu a kudun, sai lokaci ne zai nuna.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin jihar Filato a cikin shekaru 10

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin jihar Filato a cikin shekaru 10

Fiye da mutane 7,000 suka halaka a rikicin Jos a cikin shekaru 10
NAIJ.com
Mailfire view pixel