Dalilin da yasa luwadi ke karuwa a Najeriya – Gwamnatin tarayya

Dalilin da yasa luwadi ke karuwa a Najeriya – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa luwadi ta zama ruwan dare a Najeriya yayinda matasan Najeriya sun fara yinshi.

Dirakta Janar na hukumar NIA, Garba Abari, ya bayyana wannan ne a wani taron tattaunawa kan yaki da rashawa a Abuja ranan asabar.

“Wani abu mai muhimmanci da ya kamata in bayyana shine kallon tashohin kasashen waje na zama kalubale ga addinin mutanenmu da kuma al’adanmu. A yanzu ana yaudaran matasanmu da abubuwan da suka sabawa koyarwan addininmu da kuma al’adunmu.

Dalilin da yasa luwadi ke karuwa a Najeriya – Gwamnatin tarayya
Dalilin da yasa luwadi ke karuwa a Najeriya – Gwamnatin tarayya

“Zana hotuna a jiki wanda aka fi sani da ‘Tattoo’, askin yan iska, janye wando kasa da kuma penti a kai ya zama ruwan dare tsakanin matasanmu mata da maza.”

KU KARANTA: Sarauniyar kyau ta karbi Musulunci

“A yanzu matasanmu na bayani a fili cewa a hallata auren jinsi kuma suna shirin kai zanga-zangarsu majalisar dokokin tarraya domin neman da sunan hakkin dan Adam,”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel