Azumin Ramadana? Cinikin barasa ya ragu a duniya - inji wani rahoto Turawa

Azumin Ramadana? Cinikin barasa ya ragu a duniya - inji wani rahoto Turawa

- Wani sabon rahoto da ke bibiyar harkar shan barasa a faɗin duniya ya ce mutane sun rage ɗirkar ruwan giya.

- Haka zalika, cinikin barasa ya ci gaba da faɗuwa tun bara, kuma shan barasar da aka yi da tufa ya tsaya.

An samu raguwar harkokin cinikin giya a duniya da kashi 1.3% a shekara ta 2016 saboda masu sayen giyar sun ragu da kashi 1.8 cikin 100, kamar yadda ƙungiyar tattara bayanai kan harkokin barasa ta duniya, wato IWSR ta gano.

NAIJ.com ta samu labarin cewa cinikin barasar tufa ya ja da baya da kashi 1.5% bayan tsawon shekaru yana ƙaruwa.

Azumin Ramadana? Cinikin barasa ya ragu a duniya - inji wani rahoto Turawa

Azumin Ramadana? Cinikin barasa ya ragu a duniya - inji wani rahoto Turawa

Jimillar raguwar cinikin barasa a duniya ya zarta kashi 0..3 cikin 100 na faɗuwar da ake samu a cikin shekara biyar da ta wuce.

Rahoton harkokin cinikin giyar ta IWSR a bara ya gano cewa sayen barasa ya faɗi ƙasa warwas ko da yake, shan tsimammiyar giya ya ƙaru da kashi 0.3 cikin 100.

Cinikin barasa a China ya faɗi da kashi 4.2 cikin 100, sai kuma da kashi 5.3% a Brazil sai faɗuwar kashi 7.8 cikin 100 a Rasha.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Rediyo Biafara: Gwamnatin Birtaniya ta mayar da martani a kan kalaman Lai Mohammed

Rediyo Biafara: Gwamnatin Birtaniya ta mayar da martani a kan kalaman Lai Mohammed

Rediyo Biafara: Birtaniya ta mayar da martani a kan kalaman Lai Mohammed
NAIJ.com
Mailfire view pixel