Ba ni shakkar kowa a Najeriya – Al-Mustapha

Ba ni shakkar kowa a Najeriya – Al-Mustapha

- Al-Mustapha ya bayyana cewa wasu manyan mutane ne suka shirya masa gadar zare

- Al-Mustapha yace baya shakkar kowa a Najeriya

Babban dogarin tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yace dalilin daya sanya baya shakkar fadin albarkacin bakinsa shine saboda yana da gaskya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Al-Mustapha yana fadin haka ne a dakin taron Lafia Hotel dake garin Ibadan a yayin taron shekara shekara na yankin kudu maso yammacin kasar nan, a karshen makon data gabata.

KU KARANTA: Hukumar Sojin ƙasa zata gina jami’ar Sojoji a garin Biu

Yayin taron, wanda kungiyar matasan Asorodayo ta shirya shi, Al-Mustapha ya gabatar da kasida mai taken ‘Horar da matasa harkar shugabanci’, kamar yadda NAIJ.com ta jiyo daga majiyarta.

Ba ni shakkar kowa a Najeriya – Al-Mustapha

Al-Mustapha da jama'ansa

Al-Mustapha yace wasu manyan mutane ne a Najeriya suka shirya masa kutunguilar da yayi fama da shi a baya, duk don su batar da wani faifan bidiyo daya dauka dake nuna asalin wadanda suka hallaka Abiola.

Al-Mustapha ya bayyaba cewar tsohon yaronsa, Sajan Barnabas Jabila Mshiela, wanda aka fi sani da suna Sajan Rogers ya shaida ma kotu cewar biyansa aka yi don ya tsoma Al-Mustapha cikin kisan Abiola a shekarar 1998.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon makafi 4 yan gida daya

Source: Hausa.naij.com

Related news
Magoya bayan Ali Modu Sheriff na ci gaba da ficewa zaga PDP

Magoya bayan Ali Modu Sheriff na ci gaba da ficewa zaga PDP

Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP magoya bayan Ali Modu Sheriff sun shilla zuwa APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel