Jerin jihohin da ke bin ma’aikatan kudin albashi a Najeriya

Jerin jihohin da ke bin ma’aikatan kudin albashi a Najeriya

Ma’ aikatan jihohin Benue, Kogi, Abia, Oyo, Ondo da Ekiti basu karbi albashi ba gaba daya a shekaran 2017 game da binciken da BudgIT ta gudanar.

Kungiyar ta BudgIT ta bayyana wannan ne a wata jawabin da ta saki ranan Talata cewa akalla jihohi 20 ne ke bin ma’aikatansu bashi wanda ya kunshi yan fansho har watanni 36.

Lagos, Kano, Sokoto, Kaduna da wasu yan tsiraru ne kawai basu bin ma’aikata bashin albashi game da binciken.

Binciken ta nuna cewa malaman makarantun firamare, sakandare, ma’aikatan gwamnatin jiha, yan fansho ne wannan abin ya shafa.

Jerin jihohin da ke bin ma’aikatan kudin albashi a Najeriya

Jerin jihohin da ke bin ma’aikatan kudin albashi a Najeriya

“A binciken da aka gudanar, mun gano cewa jihohi 16 basu biya kudin fansho ba, 8 daga cikinsu basu biya na akalla shekara 1 ba, jihohi irinsu Imo, Taraba, da Neja kuma shekaru 2 zuwa 3 kenan basu biya.”

KU KARANTA: Aminu Masari azzalumi ne - Shema

“Bugu da kari, jihohi irinsu Kogi, Abia, Benue, Oyo, Ekiti da Ondo basu biya ma’aikatansu a wannan shekaran ba gaba daya, amma jihohi irinsu Legas da RIbas na biyan ma’aikata albashinsu lokacin da ya kamata.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naij.com

Related news
Kallo ya koma sama: Anyi taho mu gama tsakanin motar Tirela da Keke

Kallo ya koma sama: Anyi taho mu gama tsakanin motar Tirela da Keke

Mummunan haɗari: Wata babbar Mota ta mitsitstsike wani matuƙin Keke
NAIJ.com
Mailfire view pixel