Dangote ya fara rabon kayayyakin abinci na Ramadan a jihar Borno

Dangote ya fara rabon kayayyakin abinci na Ramadan a jihar Borno

- Dangote ya fara rabon kayayyakin abinci na Ramadan a jihar Borno

- Hakan na cikin kokari da ake na kyautatawa yan gudun hijira a jihar

- Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, wanda ya jagoranci shirin a garin Maiduguri babban birnin jihar ya yaba ma shugaban kungiyar Alhaji Aliko Dangote sosai da sosai

A cikin kokari da ake na kyautatawa yan gudun hijira a jihar, gidauniyar Dangote ta rabon kayayyakin abinci da sauran kayyakin amfani na watan Ramadana ga yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya cika da su a jihar Borno.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, wanda ya jagoranci shirin a garin Maiduguri babban birnin jihar ya yaba ma shugaban kungiyar Alhaji Aliko Dangote sosai da sosai, tare da bayyana gaskiyar cewa shine mutun wanda ya fi tallafawa gurin sake gina jihar Borno.

Dangote ya fara rabon kayayyakin abinci na Ramadan a jihar Borno

Dangote ya fara rabon kayayyakin abinci na Ramadan a jihar Borno

Har ila yau Injiniya Satomi Ahmed, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar, ya jinjina ma gidauniyar Dangote kan irin gudunmawa da tallafi da suke ba ‘yan gudun hijira.

KU KARANTA KUMA: Yadda ‘Yan-gaban goshin Buhari ke kokarin takawa Osinbajo burki

Da yake magana a gurin taron babbar manajan Darakta na gidauniyar, Zouera Youssoufou ta jaddada cewa gidauniyar zata ci gaba da jajircewa gurin ba jihar Borno tallafi.

Ta samu rakiyan Musa Bala, shugaban shirin, Abdulrahman Usman, da kuma Sanusi Ahmad

Kayayyakin da aka raba sun hada da Shinkafa, Alkama, Semolina, sinadarin dandano, wake, taliya, siga, da dai sauran kayayyaki da zai dauki yan gudun hijiran tsawon kwanaki 40.

NAIJ.com ta tattarom maku hotunan kayayyakin a kasa:

Dangote ya fara rabon kayayyakin abinci na Ramadan a jihar Borno

Dangote ya fara rabon kayayyakin abinci na Ramadan a jihar Borno

Dangote ya fara rabon kayayyakin abinci na Ramadan a jihar Borno

'Yan gudun hijran da suka amfana

Dangote ya fara rabon kayayyakin abinci na Ramadan a jihar Borno

Gwamnan Boro Kashi Shetimma tare Jagorar shirin a lokacin da take jawabi

Kalli wannan bidiyo da NAIJ.com ta kawo maku na Ko 'Yan Najeriya na kewar Shugaba Buhari:

Source: Hausa.naij.com

Related news
Kallo ya koma sama: Anyi taho mu gama tsakanin motar Tirela da Keke

Kallo ya koma sama: Anyi taho mu gama tsakanin motar Tirela da Keke

Mummunan haɗari: Wata babbar Mota ta mitsitstsike wani matuƙin Keke
NAIJ.com
Mailfire view pixel