2019: An bude sababbin Jam’iyyu 5 a Najeriya

2019: An bude sababbin Jam’iyyu 5 a Najeriya

– Hukumar INEC ta tabbatar da rajistar wasu sababbin Jam’iyyu

– Yanzu haka dai akwai Jam’iyyu har 45 a Najeriya

– A jiya Laraba Hukumar tayi wannan jawabi

Hukumar zabe watau INEC ta tabbatar da karin Jam’iyyu

Kwamishinan harkar zabe Adedeji Soyebi yace Jam’iyyun sun cika sharuda

Ana dai tunkarar zabe a shekarar 2019

INEC boss

Ko ya sababbin Jam’iyyun da aka bude za su kare?

Yayin da ake shirin wani zabe a shekarar 2019, Hukumar zabe ta kasar watau INEC a wani taro da tayi a Garin Kaduna ta tabbatar da cewa an yi wa wasu sababbin Jam’iyyu rajista. Akwai Jam’iyyu har 45 a Najeriya ko da da dama je-ka-nayi-ka ne kurum.

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun bude gidan rediyo

2019: PDP

Jam’iyyar adawa PDP na ta fama da rikicin shugabanci

Jam’iyyun da aka dai bude sun hada da: APDA da kuma NGP da Jam’iyyar ADPM. Har wa yau dai kuma akwai Jam’iyyar YYP da kuma ADP. Abin tambayar dai shi ne ko ya wadannan Jam’iyyu za su yi a zaben 2019?

A game da maganar zaben 2019 dai kun ji cewa ‘Yan Kungiyar Buhari Vanguard sun ce Shugaban kasa Buhari zai kara tsayawa takara a zabe mai zuwa. A cewar su Shugaban kasar ya faro aikin gyara wanda dole ya zarce domin ya kammala.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko 'Yan Najeriya na kewar Shugaban su? [Bidiyo]

Source: Hausa.naij.com

Related news
Na shirya kare kaina a gaban kotu - Sanata Hamma Isa Misau

Na shirya kare kaina a gaban kotu - Sanata Hamma Isa Misau

Na shirya kare kaina a gaban kotu - Sanata Hamma Isa Misau
NAIJ.com
Mailfire view pixel