• 365

    USD/NGN

Murza Leda: Messi yaci alwashin yin ritaya a Basalona

Murza Leda: Messi yaci alwashin yin ritaya a Basalona

- Messio yace babban burinsa yayi ritaya a Basalona

- Messi yace zai cigaba da zama a kungiyar Basalona har sai karshen zamaninsa a kwallo

Shahararren dan wasan Basalona Lionel Messi yace zai cigaba da zama a kungiyar Basalona har sai karshen zamaninsa a kwallo.

NAIJ.com ta ruwaito Messi yana fadin “Wannan shine abinda nake da muradin yi, burina inyi ritaya a Basalona”

KU KARANTA: Ban ga dalilin da zai sa na ajiye Azumi saboda harkar ƙwallo ba – Inji Ahmed Musa

Tun yana dan shekaru 13 Messi ya fara wasa a kungiyar Basalona, inda ya fara buga ma babban kungiyar yana da shekaru 17.

Murza Leda: Messi yaci alwashin yin ritaya a Basalona

Messi

Zuwa yanzu Messi ya zura kwallaye sama da 500 a kungiyar ta Basalona, kuma ya lashe gasar cin kofin kasar Sifen, La Liga sau 8, gasar zakarun nahiyar turai sau 4, sai kuma kyautan gwarzon dan kwallon duniya sau 5.

Sai dai a kakar wasan data gabata, Basalona bata samu damar lashe La Ligan ba, sa’annan ta samu nakasu a gasar cin kofin nahiyar Turai bayan da Juventus ta lallasa ta ci 3 da nema.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Related news

Tamkar yaƙin Kandak, za’a haƙa ramuka don daƙile harin Boko Haram a Maiduguri (Hotuna)

Tamkar yaƙin Kandak, za’a haƙa ramuka don daƙile harin Boko Haram a Maiduguri (Hotuna)

Boko Haram: Za’a kashe naira miliyan 50 wajen haƙa ramuka a zagaye jami’ar Maiduguri (Hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel