Jami’an yan sanda sunyi ram da samari 2 da kayayyakin hada Bam a Nasarawa

Jami’an yan sanda sunyi ram da samari 2 da kayayyakin hada Bam a Nasarawa

A yau Juma’a 9 ga watan Yuni ne hukumar yan sandan jihar Nasarawa ta damke wasu samari 2 da kayayyakin hada bama-bamai a jihar.

Kakakin hukumar, DSP Kennedy Idirisu, ya bayyanawa hukumar dillancin labaran Najeriya a Lafia cewa an damke samarin ne a karamar hukumar Loko, jihar Nasarawa.

Kana kuma hukumar yan sandan SARS ta same su da bindiga AK47 da harsasai.

DSP Kennedy Idirisu, yace a yanzu dai ana gudanar da bincike kuma sun tona asirin cewa su 6 ne masu tayar da kura a yankin.

Jami’an yan sanda sunyi ram da samari 2 da kayayyakin hada Bam a Nasarawa

Jami’an yan sanda sunyi ram da samari 2 da kayayyakin hada Bam a Nasarawa

Yace hukumar na kan bibiyan 4 da suka arce yayinda ake cigaba da gudanar da bincike domin sanin mahaifar kayayyakin hada bama-baman.

Kakakin ya kara da cewa an baiwa duk wani mazauni jihar mai makamai daman kwanaki 30 ya mika kai ko kuma an damke shi.

KU KARANTA: Tsagerun Delta sunyi barazanan kai hare-haren Bam

Ya ajiye wadannan lambobin waya ga duk wanda ke da labarin wani mai makami ya kira : 08108795930, 08112692680, 08123821571.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Rashin nada sababbin mukamai na kawo cikas a Gwamnatin Shugaba Buhari

Rashin nada sababbin mukamai na kawo cikas a Gwamnatin Shugaba Buhari

Rashin nada sababbin mukamai na kawo cikas a Gwamnatin Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel