Wai meyasa har yanzu Buhari bai cire Magu ba - Dino Melaye

Wai meyasa har yanzu Buhari bai cire Magu ba - Dino Melaye

-Dino Melaye ya caccaki fadar shugaban kasa akan Magu

-Yace da yiwuwan a kamashi ba da dadewa ba

Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattawan tarayya, Dino Melaye, ya soki fadar shugaban kasa kan rashin cire shugaban hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC. Ibrahim Magu duk da cewan majalisar taki amincewa da shi.

Ya siffanta wannan a matsayin son kai da shugaba Muhammadu Buhari yayi.

A sakon cika shekaru 2 a majalisa, sanatan ya nuna mamakinsa kan rashin cire Magu har yanzu.

Wai meyasa har yanzu Buhari bai cire Magu ba - Dino Melaye

Wai meyasa har yanzu Buhari bai cire Magu ba - Dino Melaye

A shekaru biyu da suka gabata, majalisa tayi abubuwa da yawa. Amma akwai son kai da shugaba Muhammadu Buhari yayi na barin Magu a ofis.”

KU KARANTA: An damke matasa da kayan Bam

Yayi gargadin cewa majalisa zatayi jan wuya kan duk abinda zai faru shekaru masu zuwa, saboda a shekaru 2 da suka gabata, an ci zarafin majalisa.

Dino Melaye yana nufin gurfanar da akeyiwa shugaban majalisan a kotun CCT ne.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Magoya bayan Ali Modu Sheriff na ci gaba da ficewa zaga PDP

Magoya bayan Ali Modu Sheriff na ci gaba da ficewa zaga PDP

Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP magoya bayan Ali Modu Sheriff sun shilla zuwa APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel