Dalilin da ya sa wasu yan Najeriya ke son shugaba Buhari ya mutu – Fadar shugaban kasa

Dalilin da ya sa wasu yan Najeriya ke son shugaba Buhari ya mutu – Fadar shugaban kasa

- Shugaban kasa Buhari na birnin Landan inda yake jinya amma wasu yan Najeriya ba su so ya dawo

- Laureatta Onochie ta yi ikirarin cewa harma wasu mutane kan biya shugabannin addini domin suyi ma Buhari addu’an mutuwa

- Mataimakiyar shugaban kasar ta ce duk saboda kyakyawan aiki dabuhari ke yi ne

Misi Lauretta Onochie wacce ta kasance mataimakiya na mussaman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafin zumunta ta ce wasu ‘yan Najeriya na so shugaban kasa ya mutu saboda son zuciyar su.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da 'yar jaridar da ta fadi mutuwar shugaban kasar Gabon

A wani hira da ta yi da jaridar Punch, mataimakiyar shugaban kasar ta yi magana game da lafiyar shugabna kasa da kuma tafiyarsa birnin Landan cewa wasu ‘yan Najeriya na yi masa addu’an mutuwa saboda kudirinsa na so gyara kasar zuwa tafarki mai inganci.

Onochie ta yi ikirarin cewa wasu ‘yan Najeriya ma har biyan shugabannin addini suke yi sannan kuma suna tsafe-tsafe don kawai shugaban kasar yam utu.

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com TV inda ta lissafo nasarorin shugaba Muhammadu Buhari cikin shekaru biyu

Source: Hausa.naij.com

Related news
PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2

PDP ta fadawa Shugaba Buhari ya sauke wasu Ministoci 2
NAIJ.com
Mailfire view pixel