367

USD/NGN

Shugaba Buhari ba zai dawo a karshen makon nan ba – majiyoyin fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari ba zai dawo a karshen makon nan ba – majiyoyin fadar shugaban kasa

- Majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai dawo a karshen wannan mako ba

- A baya an ce shugaban kasa Buhari zai dawo daga birnin Landan inda yake jinya

- Shugaban kasa ya bar gwamnatinsa a hannun mataimakain sa Yemi Osinbajo sannan ya tafi jinya a birnin Landan

Majiyar gwamnatin tarayyan Najeriya ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai dawo Najeriya daga birnin Landan a karshen wannan makon ba kamar yadda fadar shugaban kasar ta rahoto a baya.

Shugaban kasa Buhari ya bar kasar zuwa birnin Landan wata daya da ya wuce inda anan yake jinya da ganin likita.

KU KARANTA KUMA: Yanzu aka fara yakin: Manyan abubuwa 7 da muka gano daga sabon bidiyon Shekau

Shugaba Buhari ba zai dawo a karshen makon nan ba – majiyoyin fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari ba zai dawo a karshen makon nan ba inji majiyoyin fadar shugaban kasa

Daily Mail ta ruwaito cewa likitan shugaban kasar ya kaddamar da cewa ya zama lallai Buhari ya yi wani gwaji a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni.

A cewar majiyoyin, likita ya ce gwajin ne zai yanke shawarar ranar da zai komo kasar.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa Sahara Reporters tayi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo gida Najeriya a mako mai zuwa.

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan dawowar Buhari

Related news
Ingila tayi rashin babban Dan wasan kwallon kafa

Ingila tayi rashin babban Dan wasan kwallon kafa

Ingila tayi rashin babban Dan wasan kwallon kafa
NAIJ.com
Mailfire view pixel