Sabon salon da Boko Haram ke amfani da shi da watan Ramadana – Kwamishanan labarai

Sabon salon da Boko Haram ke amfani da shi da watan Ramadana – Kwamishanan labarai

- Gwamnatin jihar Adamawa ta bayyana sabon salon da yan Boko Haram ke amfani da shi yanzu

- Gwamnatin tace suna wayancewa da farfadiya ko kuma ciwon ciki domin tayar da Bam

- Kwamishanan labaran jihar Adamawa, Ahmad I. Sajoh, ne ya bayyana hakan

Gwamnatin jihar Adamawa ta bayyana cewa yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram suna amfani da wata sabuwar salon a wannan watan mai albarka wanda shine wayancewa da ciwon ciki ko ciwon farfadiya. Muddin suka lura mutane sun taru domin taimakawa, sai su tayar da Bam din.

Gwamnatin jihar yayinda take kira da yan Najeriya da subi a hankali, sunyi kira da kowa da kowa kan iyaye su ilmantar da yaransu kada su karbi kyauta a hannun duk wanda basu sani ba.

Sabon salon da Boko Haram ke amfani da shi da watan Ramadana – Kwamishanan labarai
Sabon salon da Boko Haram ke amfani da shi da watan Ramadana – Kwamishanan labarai

Yayinda yake magana a wata hira da manema labarai a Abuja ranan Asabar, 10 ga watan Yuni, kwamishanan yace gwamnati na daukan matakai kan dakile wannan abu amma yana akwai wuya gane shaidan a fuska.

KU KARANTA: Dan sanda a kashe dan babur a Enugu

Yace : “ Tashin Bam na farko a Yola, an ga mutane 2 na fada ne, kafi ka sani an tayar da yan kallo da Bam. Na biyun kuma sun shiga gareji ne sukace kowa ya zo yaci abinda kyauta, da mutane suka taru sai suka tayar da Bam.

“Tunda mun gane hakan zamuyi kira ga iyaye su fadawa yaransu kada su karbi komai daga hannun wadanda basu sani ba,”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel