Sanatocin Amurka sun hana siyar ma Najeriya makaman yaki

Sanatocin Amurka sun hana siyar ma Najeriya makaman yaki

- Sanatoci guda biyu yan kasar Amurka sun nuna tirjiya ga shirin siyar ma Najeriya makaman yaki

- Sanatocin sun hada da Cory Booker da Sanata Rand Paul

Wasu fitattun sanatoci guda biyu yan kasar Amurka sun nuna tirjiyarsu ga shirin siyar da makaman yaki ga Najeriya don yaki da Boko Haram da shugaban kasar Amurka Donald Trump ke yi.

Sanatocin sun hada da Cory Booker na jam'iyyar Democrat da kuma Sanata Rand Paul na jam'iyyar Republican, sun nemi a dakatar da shirin siyar wa Najeriya jiragen yaki, har sai an tabbatar da gaskiyar zargin cin zarafin dan Adam dake rataye a wuyan dakarun Sojin Najeriya.

KU KARANTA: Fasto ya musulunta bayan sauraron Tafsiri a jihar Ribas (Hoto)

Sanatocin sun bayyana ƙin amincewarsu ne a cikin wasikar da suka aikawa shugaban kasa Donald Trump ta hannun sakataren harkokin wajen kasar Amurka, Rex Tillerson.

Sanatocin Amurka sun hana siyar ma Najeriya makaman yaki

Sanata Cory Booker da Sanata Rand Paul

In da suka ce sayar wa Najeriya jiragen yaƙin na iya haifar da "Tashin hankali musamman ma a yankin arewa-maso-gabashin ƙasar ta Najeriya." Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Sanatocin sun bukaci a binciki zargin take hakkin dan Adam da aka yi a yayin harin kuskure da rundunar sojin sama ta kai a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Rann, da kuma rikicin kisan kiyashi da aka yi wa mabiya addinin Shia a Zaria.

Sai dai rundunar Sojin Najeriya ta sha musanta wadannan zarge zarge, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Sai dai kawo yanzu fadar shugaban kasar Amurka ba ta ce komai ba a kan nuna ƙin amincewar da sanatocin suka yi ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana cikin mummunan hali a garin nan

Source: Hausa.naij.com

Related news
Kungiyan Matan Gwamnonin Arewa 19 tayi alkawarin bada gudunmawar ta wajen cigaban kasa

Kungiyan Matan Gwamnonin Arewa 19 tayi alkawarin bada gudunmawar ta wajen cigaban kasa

Kungiyar Matan Gwamnonin Jihohin Arewa 19 ta dau alwashin taimakawa Gwamnatin Tarayya
NAIJ.com
Mailfire view pixel