Tambuwal ya aika Shehunnan Malamai 90 Makkah don yi ma Najeriya addu’a

Tambuwal ya aika Shehunnan Malamai 90 Makkah don yi ma Najeriya addu’a

- Jihar Sakkwato ta kammala shirin aikawa da wasu Maluma kasar Saudiya

- Za'a aika da malaman ne domin gudanar da aikin Umarah saboda wasu dalilai

Ma’aikatar kula da addini na jihar Sakkwato ta kammala shirin aikawa da wasu gagga gaggan Maluma kasar Saudiya domin gudanar da aikin Umarah saboda wasu dalilai, kamar yadda Rariya ta ruwaito.

Majiyar NAIJ.com ta bayyana cewar gwamnatin jihar ta bayyana dalilin tura malaman aikin Umarah shine domin suyi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari samun lafiya.

KU KARANTA: Rashin lafiya: Gwamnan Bauchi ya leka Saudiya neman magani

Bugu da kari ana sa ran malaman zasu yi ma jihar Sakkawato addu’an samun cigaba mai daurewa da zaman lafiya, har ma su yi ma kasa gaba daya addu’a.

Tambuwal ya aika Shehunnan Malamai 90 Makkah don yi ma Najeriya addu’a

Tambuwal

A ranar Laraba 14 ga watan Yuni ne ake sa ran Malaman zasu tashi zuwa kasa mai tsarki don gabatar da ibada da addu’o’in.

Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta dauke ma malaman dawainiyar gidajensu, inda aka baiwa kowanne malami N50,000 domin lamurran gidansa a yayin dayake Saudiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

EFCC tayi tattakin cin hanci:

Source: Hausa.naij.com

Related news
An kama wani sojan da ya gudu daga yaki da Boko Haram da laifin sata

An kama wani sojan da ya gudu daga yaki da Boko Haram da laifin sata

Wani sojan da ya gudu daga yaki da Boko Haram ya shiga hannu jami'an tsaro
NAIJ.com
Mailfire view pixel