Dandalin Kannywood: Fitaccen jarumi Suleiman Bosho zai fuskanci mummunan hukunci

Dandalin Kannywood: Fitaccen jarumi Suleiman Bosho zai fuskanci mummunan hukunci

Kungiyar ladabtar da jarumai maza da mata Moppan ta fitar da wata sanarwa a safiyar yau talata cewa: zata hukunta jarumin barkwanci Sulaiman Bosho bisa laifin dori akan abinda darakta ya umarce shi wato over role kenan.

Acewar Moppan: "Mun jima muna ganin kura kuran da Bosho Yake Yi acikin fim, mun kira shi dan ya gyara amma ya kasa gyarawa."

"Mun tuhumi daraktocin da suke da suke sa shi acikin fim amma sunce, su basu ga laifi ko munin kalamansa ba. Dan hakane muka yanke hukuncin hukunta daraktocin da kuma shi jarumi Bosho". Inji Moppan.

Dandalin Kannywood: Fitaccen jarumi Suleiman Bosho zai fuskanci mummunan hukunci
Dandalin Kannywood: Fitaccen jarumi Suleiman Bosho zai fuskanci mummunan hukunci

Legit.ng ta samu labarin cewa hukuncin da za'ayi jarumi Bosho akwai tara wanda aka ci Bosho dan wannan ya zama izna agare shi dama daraktocin da suke bashi umarnin furta kalaman da basu dace ba.

Da muka tambayi Bosho akan da wacce fuska ya kalli wannan hukunci? Sai ya amsa da cewa: "Wannan hukunci son ransu suka aikata, domin mutane sune ya kamata su gane laifin da muka aikata basu ba, domin mutane sune masu kallon mu, sune alkalai ba Moppan ba."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel