• 365

    USD/NGN

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 134 (HOTUNA)

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 134 (HOTUNA)

- An bayyana cewa Rametsi na da shekaru 134 a duniya

- Da ace an tabbatar da hakan da ta fi kowa tsufa a duniya

- Ta mutu a ranar 31 ga watan Mayu

Wata mata ‘yar kasar Afrika ta kudu da aka ce tana da shekaru 134 ta mutu.

Johanna Rametsi daga Stinkwater a Hammanskraal wajen Pretoria, ta mutu a ranar 31 ga watan Mayu.

Majiyoyi daga ‘yan uwanta sun sanar da cewa an haife ta a ranar 1 ga watan Junairu, 1883. Idan an tabbatar, wannan zai sa ta zamo wacce ta fi kowa tsufa a duniya a lokacin da take raye. Tana da takarda daga sashin kula da harkokin kasa ta Afrika ta Kudu wanda ya tabbatar da ranar haihuwar ta.

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 134 (HOTUNA)

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 134

Jeanette Ntimbane, mai kula da Rametsi, ya fada wa masu kawo rahoto cewa: “ta kasance kakata, ‘ya ta, malama ta sannan kuma ta kasance komai a gare ni. Duk da cewan na jin radadi na rashin ta a tare damu a yau ina murna da tsawon ranta kamar yadda ta so.”

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 134 (HOTUNA)

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 134

‘Yan uwan Rametsi da al’umman garin sun shirya taro don tunawa da ita a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni.

Rametsi na da ‘ya’ya 16, jikoki 78 da kuma tattaba kunne 247.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Related news

Karya ne! Jirgin Buhari baya ajiye a garin Landan - Wata majiya

Karya ne! Jirgin Buhari baya ajiye a garin Landan - Wata majiya

Karya ne! Jirgin Buhari baya ajiye a garin Landan - Wata majiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel