Addini Islama: Wasu shahararren kiristoci 2 sun musulunta a Abuja (Hotuna)

Addini Islama: Wasu shahararren kiristoci 2 sun musulunta a Abuja (Hotuna)

- Wasu mutane biyu masu addinin kirista sun musulunta a lokacin tafsirin Sheikh Isa Ali Pantami

- Mutanen da aka sani dfa Titus da kuma Hassan sun canza sunayensu zuwa Muhammad da kuma Al-Hassan

- Muhammad da kuma Al-Hassan sun ce ya dauke su dogon lokaci suna neman gaskiya, amma yanzu Allah ya bayyana masu gaskiyan

- Babban malamin ya bukaci al’ummar musulmai da a taimaka wa mutanen biyu samun aikin yi

A cewar rahotanni daga Abiyamo, wasu maza 2 kiristoci sun musulunta a lokacin tafsirin watan Ramadan na Sheikh Isa Ali Pantami.

A wajen tafsirin ne mutanen suka karbi addinin musulunci, Titus da kuma Hassan sun canza sunayensu zuwa Muhammad da kuma Al-Hassan bi da bi, wanda aka gudanar a masallacin An noor da ke birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta ruwaito cewa, mutanen biyu sun tabbatar da cewa sun dauki dogon lokaci suna neman gaskiya, amma yanzu kuma sun kasance masu farin ciki saboda a karshe Allah bayyana masu gaskiyan.

Addini Islama: Wasu shahararren kiristoci 2 sun musulunta a Abuja (Hotuna)
Sheikh Isa Ali Pantami da kiristocin da suka musulunta, Muhammad da Al-Hassan a wurin tafsir

A lokacin da yake bayyana dalilin da yasa ya musulunta, Muhammadu ya ce:

"Yanzu ya dan juma da na kasance tare da wasu musulmai kuma tsakani da Allah babu irin son da wadannan musulmai ba su nuna mini ba, ko da yake addinin mu daban-daban ne. Wannan halayen ne ya janyo hankalina sosai.”

Shi kuma Al-Hassan ya bada na shi dalilin kamar haka:

“Na dauki dogon lokaci ina neman gaskiya, yanzu kuma na samu a cikin musulunci.”

KU KARANTA: Lafiya uwar jiki: Ababan sha 3 da ya kamata mai azumi ya kauracewa (Karanta)

Da yake jawabi ga wadanda suka musulunta, Sheikh Pantami ya bukace su da su koyi rukunai na addini, ya ce: "Ina taya ku murna ga yarda kuka kadaita Allah, yanzu mun zama daya a wurin Allah, ko kuma har ma ku fini mafi alheri a wurin Allah."

Babban malamin ya kuma bukaci masu sauraro domin su taimaka musu samun aikin yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku saurari tsohon direban Bishof David Abioye na Living Faith Church wanda ya karbi

musulunci bayan ficewa daga cocin

Asali: Legit.ng

Online view pixel