• 365

    USD/NGN

Abun da dakataccen dan majalisa, Jibrin ya fada ma EFCC a lokacin tambayoyinsa

Abun da dakataccen dan majalisa, Jibrin ya fada ma EFCC a lokacin tambayoyinsa

- Dan majalisa Abdulmumin Jibrin ya amsa gayyatar hukumar EFCC a ranar Talata

- Ya amsa wasu tambayoyi da hukumar ta yi masa a kan wadanda ya zarga da zamba a kasafin kudi

- Hukumar ta ce zata gayyaci wadanda aka zarga daya bayan daya

A ranar Talata, hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ta yi ma tsohon dan majalisa Abdulmumin Jibrin, tambayoyi na kimanin sa’o’I biyar a babban ofishin ta dake Abuja.

Jibrin ya isa harabar ofishin da misalin karfe 10 na safe, inda ya tsaka har karfe 3 na rana wanda daga bisani aka nemi ya tafi, jaridar Punch ta ruwaito.

An bukaci dan majalisan da yayi cikakken bayani tsarin kasafin kudi da kuma yadda wasu daga cikin abokan aikinsa suka sanya wasu ayyuka ta wasu kamfanoninsu.

Abun da dakataccen dan majalisa, Jibrin ya fada ma EFCC a lokacin tambayoyinsa

Abun da dakataccen dan majalisa, Jibrin ya fada ma EFCC a lokacin tambayoyinsa

KU KARANTA KUMA: Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 134 (HOTUNA)

“Jibrin ya zo a ranar Talata kamar yadda aka bukata. Ya kasance tare da mu daga karfe 10 na safe har 3 na rana.

“Ya yi bayani a kan tsarin kasafin kudi da kuma yadda aka kara wasu alkalma a cikin kasafin kudin.

“Da dama daga cikin wadanda aka zarga suna da bayanai da dama da zasu yi. Zamu gayyaci wadanda aka zarga daban-daban,” cewar wani jami’I a hukumar EFCC.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Related news

Alhaji Abubakar Habu Mu'azu da ke jihar Gombe ya fitar da wasu fursunoni 30 daga gidan kaso

Alhaji Abubakar Habu Mu'azu da ke jihar Gombe ya fitar da wasu fursunoni 30 daga gidan kaso

Wani attajiri ya fitad da fursunoni 30 ta hanyar biya masu kudin tara a jihar Gombe
NAIJ.com
Mailfire view pixel