Jama’a na bautan wani yaro ‘mai bindi’ a kasar India (HOTUNA/BIDIYO)

Jama’a na bautan wani yaro ‘mai bindi’ a kasar India (HOTUNA/BIDIYO)

- An haifi wani yaro a kasar India da bindi

- Jama'a sun shiga harkar bautan wannan yaro

Wani karamin yaro dan shekara takwas mai suna Dulha Singh da aka haifa da wani abu kamar bindi a bayansa ya samu mabiya masu bauta masa.

Bindin wannan yaron ya samu asali ne daga wani tarin gashi da ya fito ma yaron a bayansa, sa’annan iyayensa sun ce yanke wannan bindi ka iya zama mummunan laifi akan wanda zai iya zuwa da mummunan sakamako.

KU KARANTA: Mutane 6 sun mutu, 20 sun jikkata a yayin gobarar bene mai hawa 27 (Hotuna)

A yanzu haka yan kauyen Amritsar, inda Dulha ke zaune da kawunsa suna tururuwa gidansa domin yi masa bauta, a yadda suke fada, sunce Dulha kwatankwancin ubangijin birai ne na addinin Hindu mai suna Hanuman.

Jama’a na bautan wani yaro ‘mai bindi’ a kasar India (HOTUNA/BIDIYO)

Yaro ‘mai bindi’

Dayake yaro Dulha na sha’awar hawa bishiya da wasa a akai, yasa ya kara tabbatar ma yan kauyen cewa lallai shine ubangijin birai na addinin Hindu.

Jama’a na bautan wani yaro ‘mai bindi’ a kasar India (HOTUNA/BIDIYO)

Yaro ‘mai bindi’

Wannan yasa yan kauyen suke ganinsa kamar wata rahama ne a garesu, shi yasa ma suke shafarsa domin samun tubarraki.

Jama’a na bautan wani yaro ‘mai bindi’ a kasar India (HOTUNA/BIDIYO)

Yaro ‘mai bindi’

Wasu kuma bindin nasa suke tabawa domin samun babban tabarraki, da karama, innarsa tace “Jama’a da daman a zuwa ganinsa a kullum, sun yi amanna shine Hanuman Ji.”

Jama’a na bautan wani yaro ‘mai bindi’ a kasar India (HOTUNA/BIDIYO)

Yaro ‘mai bindi’ tare da kawunsa da innarsa

Sai dai NAIJ.com ta ruwaito yaro Dulha baya jin komai a jikinsa, kuma baya damuwa da yadda jama’a ke son taba shi da taba bindin nasa, shi kam bai ma san dalilin da yasa jama’a ke son neman tubarraki a wajen sa ba.

Jama’a na bautan wani yaro ‘mai bindi’ a kasar India (HOTUNA/BIDIYO)

Yaro ‘mai bindi’

Ga bidiyon yaron nan:

Kalli abinda wata yarinya yar Najeriya keyi da jikinta:

Source: Hausa.naij.com

Related news
Dan sintiri ya harbe kan shi har lahira domin gwajin laya

Dan sintiri ya harbe kan shi har lahira domin gwajin laya

Dan sintiri ya harbe kan shi har lahira domin gwajin laya
NAIJ.com
Mailfire view pixel