An damke yan mata 12 sanye suna kokarin arcewa Turai

An damke yan mata 12 sanye suna kokarin arcewa Turai

Wasu yan mata mabiya addinin Kirista 7 sun badda kama ta hanyar sanya Hijabi suna kokarin shiga Turai sun shiga hannun hukumar shiga da fice wato Nigeria Immigration Service (NIS) a jihar Katsina.

Wannan ya jimmile yawan mutanen da hukumar ta damke cikin watanni 4 da suka wuce guda 40 suna kokarin bi ta Agadez na kasar Nijar sannan bi ta Libya a shiga Turai.

Yayinda aka damkesu, kontrollan Immigration a jihar, Mohammed Yaro Rabiu, yace sunyi amfani da hijabi ne domin samun daman wucewa ba tare da Ankara ba.

Dukkan wadanda aka kama yan jihar Edo ne kuma za’a mikasu ga hukumar NAPTIP domin hukunci,”.

An damke yan mata Kiristoci 12 sanye da Hijabi suna kokarin arcewa Turai ta Katsina
An damke yan mata Kiristoci 12 sanye da Hijabi suna kokarin arcewa Turai ta Katsina

Yan matan sune Dennis Igbobo, Elvis Osas, Earnest Ugiagbe, Bright John, Lucky Iyare, Gift Osagie, Godday Ruth, Ovioma Gift, Otoboh Fabour, Believe James, Endurance Idemadia da Marian Josiah.

Wasu daga cikinsu sun bayyanawa jaridar Daily Trust cewa kuncin rayuwa ne ya wajabta musu fita neman duniya.

KU KARANTA: Anyi ram da barayin kayayyakin gida a Minna

Wata yarinya mai suna Favour ta karashe karatun digirinta a ilimin jarida yace rashin aikinyi ya sata tunanin fita kasar waje samun abin yi.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel