Saurayi ya hallaka budurwarsa saboda tayi jinkirin wanke masa kaya

Saurayi ya hallaka budurwarsa saboda tayi jinkirin wanke masa kaya

- Wani mutum Mathew, ya kashe matarsa Hanna, mai dauke da juna biyu

- Masoyan sun dade sun zaman daduro kafin mummunan lamarin ya auku

Wani mutumin jihar Benuwe mai suna Mathew ya hallaka matarsa, abar kaunarsa, uwar yayansa uku, mai suna Hannah saboda wani abu da bai kai ya kawo ba, ko a ce, abinda bai taka kara ya karya ba.

Sudai wadannan matasa sun dade suna tare, amma a ranar da lamarin ya auku, Hannah wanda take dauke da ciki wata 8 ta ci duka a hannun Mathew a gidansu dake Abuja, sakamakon kin wanke masa kayansa daya bata ta wanke.

KU KARANTA: Watan Ramadana: Kwankwaso yayi rabon shinkafa

Legit.ng ta gano dalilin daya hana Hannah wanke kayan Mathew kuwa shine, a ranar ta wuni a asibiti inda taje awo, ko da ta dawo, yamma yayi, don haka sai ta dage yin wanke sai washe gari. Da gogan naka ya dawo sai ya dinga fada, ita kuwa tana bashi hakuri.

Saurayi ya hallaka budurwarsa saboda tayi jinkirin wanke masa kaya
Mathew

Daga nan ne fa ya diran mata, ya shiga dukanta, yayi mata lilisa har sai da ya hallaka ta. Sai dai makwabtan su sun bada shaidar cewa Mathew ya dade yana cutar da Hannah saboda bata haifa masa da namiji ba.

Wata makwabciyar su, Uwargida Joy ta bada shaida akan Hannah, inda tace “Hannah tayi kokari matuka wajen kulawa da yayanta mata su uku, don har aikatau ta keyi a wata makaranta ba tare da sanin Mathew ba don ta samu abin ciyar da yayanta.”

Daga karshe dai matan unguwar sun gudanar da zanga zanga inda suka kai karar Mathew ofishin yansanda, kuma tuni an kama shi, an daure shi yayin da ake gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Cin zarafi a gidan aure

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel