Labaran da ke rada cewa an kashe yan kabilar Igbo a Kaduna karya ne – El-Rufai

Labaran da ke rada cewa an kashe yan kabilar Igbo a Kaduna karya ne – El-Rufai

Bisa ga wata maganar Rediyo da e rada cewa an kashe yan kabilar Igbo a jihar Kaduna, gwamnatin jihar ta tabbatarwa yan kabilar Igbo cewa su kwantar da hankulansu.

A wata hira da yan jarida tare da shugabanin kabilar Igbo a jihar Kaduna, mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan yace, “An jawo hankalin gwamnatin jihar Kaduna cewa akwai wata maganr rediyo da ke cewa an tare wasu Igbo da ke kokarin komawa kudu kuma an kashe su da jihar Kaduna.”

“Game da cewar maganar rediyon da ke a yaren Igbo, ance an kai hari garesu a cikin mota yayinda suka nufi komawa gida.

Labaran da ke rada cewa an kashe yan kabilar Igbo a Kaduna karya ne – El-Rufai
Labaran da ke rada cewa an kashe yan kabilar Igbo a Kaduna karya ne – El-Rufai

“Mutumin da ya kirkiro wannan wanda yayi ikirarin cewa yana wajen, yayi karya cewa an kashe yan kabilar Igbo, mata da yara kuma an kona gawansu tare da motar.

“Ya bayyana karara cewa akwai wasu shaidanu masu son tayar da tarzoma a al’umma. kamar yadda kuka gano, muna nan tare da shugabancin yan kabilar Igbo a jihar Kaduna.”

KU KARANTA: Yaushe ne dare Lailatul Qadr?

Wanna labari bogi ce. Mutanen Igbo na nan cikin zaman lafiya a jihar Kaduna.

“Gwamnatin jihar Kaduna karkashin shugabancin Gwamna Nasir El-Rufai zata cigaba da kare hakkin duk wani mazaunin jihar.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel