Dandalin Kannywood: Ina murna da Rahma Sadau ta dawo harkar fim din Hausa - Aisha Tsamiya

Dandalin Kannywood: Ina murna da Rahma Sadau ta dawo harkar fim din Hausa - Aisha Tsamiya

- Tun bayan da kungiyar ladabtar da 'yan wasan hausa ta sanar cewa ta dawo da jaruma Rahma Sadau kannywood, jarumai da masu kallon fina finan hausa kowa yake faden albarkacin bakinsa.

- Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya tabi sahun takwarorinta jarumai wajen bayyana ra'ayinta akan dawowar Rahma Sadau Kannywood.

Legit.ng ta samu labarin cewa tayi wannan bayanine Instagram.

Acewar Aisha Tsamiya: "Wallahi, nayi murna da farin ciki alokacin da naji Rahma Sadau ta dawo kannywood sabida dana gaba ake gane zurfin ruwa; ma'ana, idan Rahma tayi laifi akoreta to Aisha zan iya laifi akore ni domin dan adam tara yake bai cika goma ba."

Dandalin Kannywood: Ina murna da Rahma Sadau ta dawo harkar fim din Hausa - Aisha Tsamiya
Dandalin Kannywood: Ina murna da Rahma Sadau ta dawo harkar fim din Hausa - Aisha Tsamiya

"Bayan haka duk mai kishin ma'aikatar da yake aiki to za'a same shi yana murna idan an samo sababbin ma'aikata. amma idan aka kori abokin aikinsa dole shima ya yi fargabar kada gobe shima akore shi ko akore ta.

Wannan duk misalaine don haka ina murna da Rahma Sadau ta dawo kannywood. kuma inayi mata fatan alkairi akan fim dinta maisuna RARIYA.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel