367

USD/NGN

Mutane 290,000 sukayi rijistar da shirin N-power cikin kwanaki 3

Mutane 290,000 sukayi rijistar da shirin N-power cikin kwanaki 3

- Sama da mutane 290,000 sukayi rijista a shafin yanar gizo na shirin samar da aikin gwamnatin tarayya na Npower.

- Babban mai taimakawa Shugaban kasa kan samar da aiyukan yi, Afolabi Imoukhuede, ya bada wannan bayanin lokacin da yake ganawa da wadanda suka amfana da shirin a Benin babban birnin jihar Edo.

A cewarsa mutane 200,000 ne da suka gama makaranta suka shiga cikin kason farko na shirin yayin da za a kara daukan mutane dubu 300,000 a kaso na biyu.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya kuma koka kan yadda ake shigar da bayanai ba dai-dai ba yayin da matasan suke shigar da bayanansu a shafin yanar gizon.

Mutane 290,000 sukayi rijistar da shirin N-power cikin kwanaki 3

Mutane 290,000 sukayi rijistar da shirin N-power cikin kwanaki 3

Imoukhuede yace gwamnati tana kashe naira biliyan 6 a duk wata wajen biyan mutanen da suke karkashin shirin inda yace wannan ba karamin kudi bane.

Ya kara da cewa a wannan karon za afi bada fifiko ga mutanen da suke zaune a karkara domin maganin kwararowar mutane cikin birane.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Related news
Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari na ganawa da mahaifinsa
NAIJ.com
Mailfire view pixel